<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>439</hymn_number>
<title>Kana da Kuɗi LW439</title>
<lyrics>[V1]
 1) In kana da kuɗi, sai girman kai
 Kana dubin fa ka fi kowa
 Wanda ba shi da kana dubin ka fi shi
 Tuna fa ƙarshen mu guda ne.

[V2]
 KORUS
 Mine ne ka samu oh ya ɗan Adam
 Wanda Allahnmu bai baka ba
 Domin haka kawas da girman kai
 Ka miƙa kanka ga Allah.

[V3]
 2) In kana da illimi sai girman kai
 Kana dubin kowa jahili
 Wanda ba shi da illimi ka raina shi
 Tuna fa ƙarshen mu guda ne.
 Korus

[V4]
 3) In kana da baiwa sai girman kai
 Kana doro kana takama
 Wanda ba shi da kana dubin ka fi shi
 Tuna Ubangijinmu guda ne.
 Korus

[V5]
 4) Allah ya bada baiwa ga kowane ɗayanmu
 Domin aikinsa ya ci gaba
 Abin da Allah ya baka ka yi aikinsa da shi
 Gama Ubangijinmu guda ne.
 Korus</lyrics>
</song>